Ta yaya za mu daina cin abinci fiye da ƙima?

Asalin hoton, Getty Images
A wasu ƙasashen duniya, a shekara 50 ko sama da haka da suka gabata, ana samun ƙaruwar mutane masu fama da ƙibar da ta wuce ƙima.
Amma yaya za mu kasance cikin ƙoshin lafiya ba tare da yawan cin abinci ba? musamman ganin yadda kusan kullum kamfanonin cimaka suke ta ƙara sana'anta sababbin nau'ukan abinci masu daɗi da jan hankali?
Dr. Lisa Young ta jami'ar New York ta bayyana wa BBC cewa: "idan akwai shagon indomie mai tsada da kuma wani shagon mai arha, mutane za su fi sha'awar zuwa waje mai arha su saya," in ji ta.
Ta ƙara da cewa, "abinci ya fi arha. Kuma idan abinci ya fi arha, kowane ɓangare ya fi ƙaruwa wato mai sayarwa ya samu kasuwa, mai saya kuma ya ƙoshi da kuɗi kaɗan," in ji ta
Dr. Marle Alvarenga na jami'ar São Paulo, ya ce ana ganin irin wannan canjin na yanayi cimaka a ƙasashe masu tasowa.
Shin mun fi cin abinci idan yana da yawa?
Masana sun ce akwai hujjojin da ke nuna cewa mutane sun fi cin abinci mai yawa idan sun ga akwai abincin mai yawa.
Wani bincike da aka yi, ya yi ƙiyasin cewa mutane suna cin ƙarin kashi 35 na abinci idan akwai abincin mai yawa.
"Ba maganar ƙarasa abincin da aka saka maka ba ne ake yi, saboda akwai waɗanda ba su da saurin cin abinci. Amma mun san idan girman kwanon abinci ya ƙaru, cin abincin ma yana ƙaruwa," in ji Farfesa Lenny Vartanian, na jami'ar New South Wales a birnin Sydney na ƙasar Australia.
Farfesan ya ce babbar matsalar ita ce da wahala a iya gane haƙiƙanin abin da mutum ya kamata ya ci, domin a lokuta da dama jikinmu ba ya nuna mana alamar da ta dace.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙaramin kwanon abinci zai taimaka?
A baya an yi tunanin cewa idan aka rage girman kwanon abinci, za a samu sauƙi wajen rage ci saboda dole abinci ƙadan za a zuba. Sai dai bincike ya nuna cewa ba hakan lamarin yake ba.
Farfesa Vartanian ya ce, "girman kwanon abinci ba shi da alaƙa da yanayin cin abincin mutum. Babban abin da ke da amfani shi, shi ne akwai abincin ko babu kawai," in ji shi.
Matuƙar akwai abinci, mutane sukan ci mai yawa ba tare da la'akari da girma ko ƙanƙantar kwano ba.
Yaya za a rage ci?

Asalin hoton, Getty Images
Masana sun ce babban abin da ya fi dacewa mutum ya yi shi ne fahimtar lokacin da yake jin yunwa, tare da fahimtar lokacin da ya fi dacewa ya ci abinci.
"Mutane ba su cika la'akari da abin da ke cikin kwano ba, kuma ba su cika fahimtar asalin lokacin da suke buƙatar cin abinci ba. Haka kuma wasu ba su cika gane lokacin da suka ƙoshi ba," in ji Dr Lisa Young na jami'ar New York University.
A game da tsarin da ya kamata a bi wajen cin abinci, Dr. Marle Alvarenga ya ce, "shawarata ita ce a riƙa kula sosai da samfurin abinci da girmansa. Wannan zai taimaka matuƙa."
Cimakan maƙulashe
Dr Young ya ce, "idan kana cin abincin da aka noma masu ɗauke da sinadaran dusa da ƴaƴan itatuwa, yawan abin da ka ci bai cika zama matsala ba saboda haɗi ne mai inganci kuma ba su da illa ga lafiya."
Amma idan abinci ne da aka sana'anta ne a kamfanoni, a ciki akwai sinadaran da ke ciki, nan ne akwai abin lura.
"Za ka ji mutum ya ce ya ci ƙaramin kwano na abinci da safe, amma idan ka kwatanta abincin, za ka ga ya ci kusan niki uku na abin da wani ya ci a lokaci guda," in ji ta.












