Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 04/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 04/06/2026.

Skip Bidiyo and continue reading
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx
  • Nafiu Gombe
  • Mace da ƴarta mai lalaurar Autism
  • wata mata
  • BBC reporter

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi

  1. Yadda kama mai fyaɗe a Faransa ya tayar da hargitsi a Faransa

    An samu hargitsi da tashin tashina a Faransa bayan da aka gano cewa mutumin da ake zargi da ɓatar da wata yarinya ƴar shekara 11, a baya an taɓa zargin sa da cin zarafin ƙananan yara ta hanyar lalata, amma ba a ɗauki mataki ba.

    Yarinyar mai suna Lyhanna ta ɓata a ranar juma'ar da ta gabata kusa da ƙauyen Fleurance da ke kudu maso yammaci, kuma an yi mata gani na ƙarshe ne a lokacin da take shiga motar wani mutum.

    An kama wani mutum mai shekara 41 da ake zargi da ɓatar yarinyar. Mutumin ya amince cewa ya rage wa yarinyar hanya, amma a cewarsa ya ajiye da a wani wurin yin ninkaya.

    Masu gabatar da ƙara sun ke an zargi mutumin sau biyu da laifin yi wa ƙananan yara biyu fyaɗe.

  2. Rasha ta caccaki Amurka kan yaƙin Ukraine

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan harkokin wajen Rasha ya caccaki takwaransa na Amurka kan kalaman da ya yi na cewa dukkanin ɓangarorin da ke yaƙin Ukraine sun ƙi bada haɗin kai domin cimma matsaya.

    Sergei Lavrov ya ce kalaman da Marco Rubio ya yi a jiya Laraba sun zo mishi bambarakwai, inda ya dage cewa a yayin tattaunawar da aka yi a watan Agustan bara a Alaska, shugaba Putin ya amince da buƙatun da Amurka ta gabatar na kawo ƙarshen yaƙin.

    Amma har yanzu kofar tattaunawa tsakanin Moscow da Washington a buɗe ta ke.

    Wakilin Putin na Kirill Dmitriev ya ce har yanzua ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Rasha da Amurka kan takunkumin tattalin arziƙi da aka ƙaƙabawa ƙasar.

  3. Trump ya caccaki ƴan majalisar kan ƙudurin hana shi yaƙar Iran

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Trump ya caccaki ƴan majalisar wakilai kan amincewa da wani kuduri na jeka na yi ka da ke taka masa birki kan yaƙin Iran.

    Ƴan majalisar daga jam'iyyar Republican hudu sun goyi bayan 'yan Democrats wajen amincewa da wannan ƙuduri, wanda ya umarci Shugaban ya janye sojojin Amurka daga Iran, ko kuma ya nemi amincewar majalisun dokokin kasar kan ci gaba da yakin.

    A yanzu haka rinjayen ƴan majalisar da ba sa jin daɗin yaƙin da ake yi, kuma suka zaɓi su bayyana rashin amincewarsu ta hanyar kaɗa kuri'a.

    Mista Trump ya bayyana matakin majalisar a matsayin ta rashin kishin ƙasa, inda ya ce sun yi hakan ne a yayin da ake gab da cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin.

  4. 'Ba mu yi laifi ba barin Amurka ta gina cibiyar kula da masu Ebola a Kenya'

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Kenya, William Ruto, ya ce gwamnatinsa ta yi "abin da ya dace" inda ta bai wa Amurka damar gina cibiyar killace masu cutar Ebola a ƙasar.

    Ya ce ƙin amincewa da samar da cibiyar, wadda Washington za ta gina da kuɗinta, zai zama wani abu na rashin mutunci.

    Kalaman nasa na zuwa ne duk da zanga-zanga da kuma umarnin kotu na hana gina ta.

    Za a gina cibiyar ne mai gadaje hamsin a kusa da birnin Nanyuki da ke tsakiyar ƙasar.

    Ɗaruruwan mutane ne suka kamu da cutar ta Ebola a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo, kuma har ta bazu zuwa makwabciyarta Uganda.

  5. Jam'iyyar PRP ta nemi Tinubu ya yi murabus

    ..

    Asalin hoton, Bayo Onanuga/X

    A Najeriya, jam’iyyar PRP ta buƙaci shugaba Tinubu ya yi murabus saboda kasa kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasar. ‎

    Shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ya yi zargin cewa matsalar tsaro ta ƙara ta’azzara a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, inda yace hare-hare da sauran laifuka sun ci gaba da ƙaruwa.

    Ya ƙara da cewa mutane da dama na fadawa hannun masu aikata laifi ba tare da la’akari da matsayinsu ko shekarunsu ba.

    Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da hare-hare ƴan bindiga da sace-sace ke ƙara ta'azzara, inda yanzu haka suke ƙara ƙamari a kudu maso yammacin ƙasar.

  6. Pakistan ta zargi India da amfani da ruwa a matsayin makami

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Pakistan ta ce India na amfani da ruwa a matsayin makami, bayan da ta sanar da wasu sabbin ayyuka da za ta yi da za su shafi wani kogi mai suna Chenab da ƙasashen biyu ke amfani da shi.

    Ma'aikatar harkokin wajen Pakistan ta ce duk wani mataki da ke barazana ga samar da ruwa da abinci na Pakistan ya haramta, kuma ba za a lamunta ba.

    A shekarar alif dari tara da sittin, maƙwaftan sun sanya hannu kan wata yarjejeniya mai suna Indus Water Treaty, domin su riƙa amfani da ruwan kogunan da suka ratsa daga India zuwa Pakistan.

    A bara, Delhi ta ce za ta dakatar da yarjejeniyar, inda ta ke zargin Islamabad da kai mummanar hari kan masu yawon buɗe ido a Kashmir, har ya kai ga ministan cikin gida ya yi barazanar hana Pakistan ruwa.

  7. Ta yaya za mu daina cin abinci fiye da ƙima?

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    A wasu ƙasashen duniya, a shekara 50 ko sama da haka da suka gabata, ana samun ƙaruwar mutane masu fama da ƙibar da ta wuce ƙima.

    Amma yaya za mu kasance cikin ƙoshin lafiya ba tare da yawan cin abinci ba? musamman ganin yadda kusan kullum kamfanonin cimaka suke ta ƙara sana'anta sababbin nau'ukan abinci masu daɗi da jan hankali?

    Dr. Lisa Young ta jami'ar New York ta bayyana wa BBC cewa: "idan akwai shagon indomie mai tsada da kuma wani shagon mai arha, mutane za su fi sha'awar zuwa waje mai arha su saya," in ji ta.

    Ta ƙara da cewa, "abinci ya fi arha. Kuma idan abinci ya fi arha, kowane ɓangare ya fi ƙaruwa wato mai sayarwa ya samu kasuwa, mai saya kuma ya ƙoshi da kuɗi kaɗan," in ji ta

    Dr. Marle Alvarenga na jami'ar São Paulo, ya ce ana ganin irin wannan canjin na yanayi cimaka a ƙasashe masu tasowa.

  8. Kotu ta umarci Sowore ya kare kansa kan ɓatanci ga Tinubu

    ..

    Asalin hoton, Sowore/X

    Mai shari'a Mohammed Umar na babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, ya umarci ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore da ya kare kansa dangane da zargin da ake yi masa da ɓata sunan shugaba Bola Ahmed Tinubu.

    A lokacin shari'ar mai shari'a Umar ya yi watsi da roƙon lauyan Sowore, Marshall Abubakar na neman a ɗage shari'ar har zuwa lokacin da kotun za ta koma daga hutu.

    Alƙalin ya kuma bayar da umarnin ci gaba da sauraron shari'ar a kullum kuma za a fara dada ranar Juma'a 5 ga watan Yuni, a lokacin da ya zamar wa wanda ake zargin ya kare kansa.

    Hukumar farin kaya ta DSS ce dai take tuhumar Sowore wanda ɗan jarida ne ɓata wa shugaba Tinubu suna a shafukansa na X da Facebook.

  9. Jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya ya mutu a harin Lebanon

    Wani jami'in wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya ɗan asalin Serbia ya mutu, wasu biyu ƴan Sipaniya kuma sun jikkata a Lebanon.

    A ranar Laraba ne aka kai harin bam kan sansanin jami'an Majalisar da ke kudu maso gabashin ƙasar.

    An kwashe lokacin ana gwabzawa tsakanin Hezbollah mai samun goyon bayan Iran da kuma dakarun Isra'ila a yankin.

    Tawagar wanzar da zaman lafiyar ba ta ambaci ko wane ɓangare ne ke da alhakin kai mata hari, amma ta ce ta soma gudanar da bincike.

    Isra'ila ba ta cika ke amfani da irin makamin wajen kai wa Hezbollah hari ba.

  10. Keir Starmer ya zargi Elon Musk da haifar da rabuwar kai a Birtaniya

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Keir Starmer ya zargi Elon Musk da ƙoƙarin kawo rarrabuwar kai a Birtaniya, sakamakon fushin da ake ta nunawa game da yadda ƴan sanda suka tafiyar da batun kisan wani ɗalibi farin fata da wani mabiyin addinin Sikh ya yi.

    Fira ministan Birtaniya ya ce Musk na ta yin shishigi cikin siyasar Birtaniya. Mista Musk na ta wallafa rubuce-rubuce a shafukansa kan lamarin, inda yake ta yaɗa kalaman da wasu masu tsattsaurar ra'ayi suka yi, har ma ya yi tayin samar da kuɗaɗen da za a yi amfani da su wajen gurfanar da ƴan sanda gaban shari'a.

    An sanya wa Henry Nowak ankwa sannan aka kama shi a yayin da ya ke kwance cikin jini bayan an caka masa wuka.

    Mutumin da ya kashe shi ya masa kage inda ya zarge shi da nuna masa wariyar launin fata.

    Lamarin ya yi sanadiyyar samun tashin tashina a Southampton, inda aka yi kisan.

  11. Hare-haren Isra'ila sun kashe Falasɗinawa 11

    Jami'an Lafiya da shaidu a Gaza sun ce Falasɗinawa aƙalla goma sha ɗaya sun mutu, yayin da gommai suka jikkata a hare-haren da Isra'ila ta kai a ranar Alhamis.

    Ma'aikatan lafiya sun shaida wa BBC cewa wani jirgin saman yaƙi na Isra'ila ya kai hari kan gidaje huɗu a birnin Gaza.

    Wakilin BBC ya ce cikin waɗanda rahotanni suka bayyana an kai wa hari, har da wani kwamnadan Hamas, wanda aka hallaka tare da matarsa da yaransa uku.

    Isra'ila ta kai hare hare da dama a Gaza, duk da tsagaita wutar da aka cimma a watan Oktoban da ya gabata, da Amurka ta jagoranta, inda ta ke zargin Hamas da ci gaba da samun makamai da sake gina dakarunta.

  12. Isra'ila ba za ta zauna lafiya ba muddin ta ci gaba da kai mana hari - Hezbollah

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban ƙungiyar Hezbollah mai samun goyon bayan Iran, ya ce duk wata yarjejeniya da za a cimma tsakanin Lebanon da Isra'ila tamkar sun miƙa wuya ne ko kuma an ci su da yaƙi.

    Sanarwar da Naim Qassem ya fitar za ta iya kawo tsaiko ga yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka ke jagoranta, wadda shugaban Labanon, Joseph Aoun, ya bayyana a matsayin dama ta ƙarshe ta samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

    Isra'ila ta dage cewa za ta iya ci gaba da yaƙin da take yi ta ƙasa a Kudancin Lebanon.

    Ita kuwa Hezbollah ta ce ba za a taɓa samun zaman lafiya a arewacin Isra'ila ba, muddin aka ci gaba da kai hari a kauyukan Lebanon.

    Wakilin BBC ya ce Hezbollah na kallon shirin tsagaita wutar a matsayin tozarci ga Lebanon.

  13. Ƴansanda sun ƙaryata rahoton sakin ɗaliban Oyo

    ...

    Asalin hoton, @OyoPoliceNG/X

    Rundunar ƴansanda a jihar Oyo ta musanta rahotannin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta inda ake zargin cewa ƴanbindiga suk sako ɗalibai da malaman da suka sace a ƙaramar hukumar Orire a jihar Oyo.

    Rundunar ta bayyana haka a sanarwar da kakakinta, DSP Ayanlade Olayinka ya sanyawa hannu inda ta ce rahoton ƙarya ce tsagwaranta.

    Cikin sanarwar, rundunar ta kuma bai wa al'ummar jihar ta Oyo tabbaci cewa ana ci gaba da ƙoƙari na ganin an kuɓutar da ɗaliban da malaman.

    Rundunar ta kuma yi kira ga mazauna jihar da su guji jita-jita su kuma nemi sahihan labarai daga ƴansanda.

    Lamarin hare-haren 'yan bindiga da satar mutane don neman kuɗin fansa sun fi ƙamari ne a yankin arewacin Najeriya, inda ba kasafai aka saba ganin hakan ba a kudancin ƙasar, wadda ke fama da matsaloli na tsaro.

    A baya-bayan nan ita ma dai jihar ta Oyo na fuskantar matsalar tsaron daga gungun masu aikata laifi.

  14. An yi musayar wuta kan rikicin zaɓe a Somaliya

    ....

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Dakarun gwamnati da mayaƙa sun yi musayar wuta a Mogadishu, babban birnin Somaliya sakamakon rikici game da jan ƙafa wajen gudanar da zaɓe.

    Wa'adin Shugaba Hassan Sheikh Mohamud kan karagar mulki ya zo ƙarshe ranar 15 ga watan Mayu amma an tsawaita shi da shekara ɗaya.

    Ɓangaren hamayya ya ce hakan ya saɓa da kundin tsarin mulki inda kuma suka kira a gudanar da zanga-zanga a yau Alhamis.

    Rahotanni sun ce an ji ƙarar harbe-harbe a wasu yankuna na babban birnin har zuwa cikin dare, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.

    Ƴansanda sun ce suna aiwatar da gagarumin samame ne kan mayaƙa masu riƙe da makamai da suka kai hare-hare a yankunan.

    Bayan cikar wa'adin shugaban ƙasar ne gwamnatin tarayya da ɓangaren hamayya suka shiga tattaunawa sai dai sun gaza cimma matsaya.

  15. An kashe Falasɗinawa 11 a hare-haren Isra'ila

    Jami'an lafiya da shaidu a Gaza sun ce an kashe Falasɗinawa aƙalla 11 inda wasu da dama suka ji rauni a hare-haren da Isra'ila ta kai a ranar Alhamis.

    Likitoci sun shaida wa BBC cewa wani jirgin Isra'ila ya kai hari kan aƙalla gidaje huɗu a birnin Gaza.

    Daga cikin waɗanda rahotanni ke cewa harin ya shafa akwai wani kwamandan Hamas wanda aka kashe tare da mai ɗakinsa da kuma ƴaƴansa uku.

    Isra'ila ta kai hare-hare a Gaza duk da yarjejeniyar tsagaita wuta ta watan Oktoba da Amurka ta shiga tsakani, inda take zargin Hamas da sake haɓaka sojojinta.

    Fiye da mutum 940 aka kashe tun lokacin, a cewar ma'aikatar lafiyar Falasɗinu.

  16. Ƴanbindiga sun sace ɗaliban kwalejin fasaha a Zamfara

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar ƴansanda a Najeriya ta ce ƴanbindiga sun sace wasu ɗaliban kwalejin fasaha ta tarayya da ke Ƙaura Namoda a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar.

    An sace ɗaliban bakwai da sanyin safiyar jiya Laraba daga gidan da suka zaune a wajen yankin.

    Kakakin rundunar ƴansandan jihar Yazid Abubakar cikin wata sanarwa ya ce maharan sun kutsa gidajen ɗaliban inda kuma suka yi awon gaba da wasu daga cikinsu.

    Sanarwar ta ƙara da cewa an tuntuɓi sojoji da jami'an da aka tura yankin sai dai ƴanbindigar sun riga sun tsere kafin jami'an tsaro su isa wajen.

    "Ɗaya daga cikin ɗaliban da aka sace ya samu tserewa kuma tuni aka miƙa shi ga hukumomi yayin da ake ƙara ƙoƙari na gano ragowar mutum shida," in ji sanarwar.

    Rahotanni sun ce jami'an tsaro tuni suka fara samame domin gano inda ƴanbindigar suke kuma zuwa yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin.

    Jihar Zamfara da Kebbi da Katsina masu maƙwabtaka na fuskantar ƙaruwar hare-hare a baya-bayan nan sakamakon ayyukan ƴanbindiga.

  17. Gwamnatin Najeriya na son masu sola su riƙa sayar mata da lantarki

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kula da wutar lantarki a Najeriya NERC ta fara amfani da wani tsari wanda zai bai wa masu amfani da sola damar siyar wa hukumomi lantarki.

    NERC ta bayyana haka ne a shafinta na X inda ta ce "idan sola ɗinku na samar da lantarki fiye da buƙatarku, za ku iya sayar wa kamfanonin rarraba lantarki ƙarin wuta kuma a biya ku kuɗi"

    A cewar NERC, wannan tsarin shi ake kira Prosumer a Turancin Ingilishi wato inda kwastoma zai kasance mai amfani da kuma samar da lantarki.

    Sai dai akwai ƙa'idoji da ke tattare da tsarin da suka haɗa da dole ka zama kwastoma a kamfanin rarraba lantarki sannan kuma dole sola ɗin da mutum ya saka ta zama mai ƙarfin 50kwp.

    Kazalika, dole sai mutum ya samu izini daga kamfanin rarraba lantarki bugu da ƙari kuma sai ka sa hannu kan yarjejeniya ta sabon tsarin sannan kuma mutum sai ya yi rajista da NERC.

    Sanarwar ta ce tsarin bai shafi gidaje masu amfani da matsakaicin sola ba.

  18. Isra'ila da Lebanon sun yarda su aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Isra'ila da Lebanon sun amince da sabunta ƙwarya ƙwaryar yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma ƙirƙirar wasu yankuna na tsaro na gwaji - inda sojojin Lebanon za su karɓi iko da su.

    Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa ta haɗin gwiwa daga ɓangarorin biyu bayan tattaunawa da Amurka da ta shiga tsakani a Washington.

    Wakiliyar BBC ta ce ɓangarorin biyu sun ce sabuwar yarjejeniyar ta dogara ne akan dakatar da buɗe wuta da Hezbollah ke yi gaba daya da kuma kawo ƙarshen dukkan ayyukansu a yankunan da ke kudancin Lebanon.

    Tuni dai Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran ta yi watsi da matakin.

  19. Majalisar dokokin Amurka ta buƙaci Trump ya daina yaƙi a Iran...

    Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar wakilai ta Amurka ta kaɗa ƙuri'a inda ta umarci Shugaba Donald Trump ya janye sojojin Amurka daga yakin Iran, ko kuma ya nemi amincewar majalisun dokokin ƙasar kan ci gaba da yaƙin.

    Ƴan majalisar daga jam'iyyar Republican huɗu sun goyi bayan ƴan Democrats wajen amincewa da wannan mataki wanda yanzu zai wuce zuwa majalisar dattawan ƙasar.

    Matakin da aka ɗauka dai ya kasance na je-ka na yi-ka ne a yayin da shugaban ƙasa ke da ikon hawa kujerar na-ƙi a kan duk wani hukunci ko matakin da ya ga zai ka wo masa matsala a shugabancinsa.

    Wannan shi ne matakin na baya-bayan nan na kara nuna adawa da matakin Trump din a kan Iran, daga cikin jam'iyyarsa ta Republican.

  20. Barka da warhaka!

    Barka da zuwa shafin BBC Hausa na kai-tsaye wanda ke kawo muku labaran duk abubuwan da ke faruwa game da yaƙin Iran da kuma muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da saurarn sassan duniya a wannan rana ta Alhamis - ta-bawa, ranar samu.

    Za ku iya yin tsokaci a shafukanmun na sada zumunta: facebook, X, instagram, YouTube sai kuma zaurenmu na WhatssApp.