Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin wajibi ne daina aski da yanke farce ga mai layya?
Daga cikin batutuwan da ake yawan tattaunawa da zarar an kusa shiga watan Dhul-Hijjah akwai hukunce-hukuncen layya da darajar kwanaki 10 na farkon watan da ibadun da suka kamata a yi.
Daga cikin ibadun da ake yi akwai maganar cewa duk wanda zai yi layya bai kamata ya yi aski ko yanke farce ba ga namiji, da kuma kitso ga mace har sai bayan Sallah, wato bayan yanka.
Wannan magana tana cikin maganganun da malamai suke yawan tattaunawa, har ta zama wasu na ganin rashin bin dokar na iya ɓata aikin ibadar ta layya da ake yi a lokacin babbar Sallah.
Akan umarci mutane da su yi aski, su yanke kumba da kuma rage duk wani gashi na jikinsu kafin kamawar watan Dhul-Hijja, idan kuma ba haka ba, to ba za su iya yanke gashin ko kumnar tasu ba har sai bayan an sauko idi a ranar 10 ga watan na Dhuk-Hijja.
To amma mece ce gaskiyar batun?
'Yadda abin yake'
Sheikh Hussaini Zakariyya, malamin adinin Musulunci ne a Najeriya, ya bayyana cewa akwai bambancin hukuncin a farkon zuwan addini da kuma yadda hukuncin ya koma a ƙarshen rayuwar Annabi Muhammadu.
A cewarsa, "Babu shakka wannan magana kusan kowace shekara sai ta taso saboda mutane suna da mantuwa sosai a kan wannan hukunci," in ji shi, inda ya ƙara da cewa malamai sun daɗe suna tattauna batun.
"Hukuncin ya kasu kashi biyu ne, akwai farkon Musulunci da kuma daga baya-baya wato ƙarshen rayuwar Annabi Muhammad."
Ya ce a farkon Musulunci ne aka ce da zarar watan Dhul-Hijja ya tsaya ba a son mai layya ya yi aski da saisaye da yanke farce ko yanke wani abu na jikinsa da kitso ga mata da sauran su da aka haramta wa mai aikin hajji.
Malamin addinin ya bayyana cewa matar Manzon Allah Ummu Salama da sahabi Abdullahi Bn Abbas sun ruwaito hadisin, kuma ya ƙara da cewa akwai ruwayoyin a cikin littafan hadisin Buhari da Muslim.
Sai dai malamin addinin ya ce a ƙarshen rayuwar Manzon Allah abubuwa sun sauya.
"A duk shekara Manzon Allah yana aika abin layyarsa zuwa Makka a yanka, a raba wa alhazai domin layya ko sadaka a Makka ta fi lada," in ji shi.
Sheikh Hussaini ya ce matar Manzon Allah, Aisha ta ce "na kasance ina tufka alamun da za a saka wa abin layyarsa sai ya karɓa ya ɗaura," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa ta ce bayan ya kora abin layyar ba ya barin duka abin da mai aikin hajji yake bari.
“Yana saduwa da iyalinsa, yana sanya turare, yana aski, yana sanya turare kuma yana yanke farce”.
"Na tattara littafai sun kusa 20 kuma dukkansu sun tabbatar da cewa an canja wannan hukuncin," in ji shi, kamar yadda akan canza wasu dokoki a Kur'ani .
"Saboda haka an samu hadisi ya soke na farko. Amma malamai da yawa sun riga sun rubuta sosai kuma sakon ya yi nisa, sai jama'a suka ruɗe. Amma idan mutum ya bincike zai gane yadda hukuncin yake a yanzu," in ji shi.
Ya ƙara da cewa ko a game da batun askin da yanke farce da sauransu, ''malamai da suke cewa kada a yi sun kasu kashi biyu akwai masu cewa haramun ne akwai masu cewa makaruhi.''
Saboda haka malamin ya ce hadisai da bayanai da aka samu sun nuna cewa an sauya dokar, saboda haka ya halsta mutum ya yi aski da duk abin da ya halasta.