Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
Za mu baiwa sojojinmu wadatattu makamai don yaƙi da 'yan ta'adda -Tinubu
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sauran sassan duniya, Asabar 11/04/2026
'Na san an samu kuskure': Iyalan da suka haihu da maniyyin da ba nasu ba
Wasu iyalai bakwai sun yi imanin cewa an yi amfani da maniyyi ko ƙwayayen da ba nasu ba yayin aikin dashen ɗantayi.
Mutane 5 da ke wakiltar Amurka da Iran a tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin Iran
Yayin da wakilan Amurka da Iran suka isa birnin Islamabad domin tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin Iran da Amurka, hankula sun koma kan su wane ne wakilan ɓangarorin biyu.
Su wane ne masu ɗaukar nauyin ta'adanci a Najeriya?
A baya dai Najeriya ta sanar da matakin ladabtarwa kan wasu mutanen da kamfanoni, kamar yadda kwamitin tsaro na majalisar Dinkin Duniya ya gindaya, kuma cikin matakin da aka ɗauka harda na rufe asusun ajiyar su da kuma taƙaita tafiye-tafiye gare su.
Me ya sa Boko Haram ke kai wa manyan sojoji hare-hare?
Ƙaruwar hare-haren alama ce da ke nuna cewa ƙungiyoyin na ci gaba da samun ƙarin makamai.
Wace dama Iran za ta iya samu yayin tsagaita wuta?
Masu ra'ayin mazan jiya a ƙasar ta Iran ba su ji daɗin tsagaita wutar ba kuma rahotanni daga Tehran sun nuna cewa an riƙa ƙona tutocin Amurka da Isra'ila bayan sanar da yarjejeniyar.
Muna shirya kayan yaƙi ko da Iran za ta yi mana tutsu a yarjejeniya - Trump
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kan yaƙin Iran da kuma muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Juma'a 10 ga watan Afrilun 2026.
Martanin da Abba Kabir ya mayar wa Kwankwaso
A karon farko gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya mayar da martani ga tsohon ubagidansa na siyasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso tun bayan raba gari da mutanen guda biyu suka yi.
Tsagaita wuta: Wurare 5 da sharuɗɗan Iran suka ci karo da na Amurka
Duka ɓangarorin biyu sun gabatar da sharuɗɗan kawo ƙarshen da aka shafe kimanin kwana 40 ana gwabzawa.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Safe, 05:29, 12 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 11 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 11 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 11 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Wasanni
KAI TSAYE, Sakamakon wasannin ƙarshen mako: Madrid ta sake gamuwa da cikas
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga ranar Talata 7, zuwa Asabar 11 ga watan Afrilun 2026.
Wane mai tsaron raga ne ya fi tashe a wannan lokaci?
David Raya da Manuel Neuer sun nuna hazaƙa a wasannin gasar Champions League da ƙungiyoyinsu suka buga a baya-bayan nan - to amma ko suna cikin mafiya hazaƙa a duniya?
Arsenal da Chelsea da Man U da Real Madrid na son Smit, Carrick na daf da zama kocin Man U
Chelsea na iya sayar da Enzo Fernandez a bazara , Arsenal, da Chelsea, da Man U da Real Madrid na zawarcin Smit.
Manyan ƙungiyoyi na zawarcin Rogers, Madrid ta matsa kan Olise
Liverpool da City da Arsenal sun ƙwallafa rai kan Cameroon, Juventus na kara samun kwarin gwiwa a kokarin daukar golan Brazil Alisson Becker daga Liverpool.
Dortmund ta nace wa Sancho, Tottenham ta matsa a kan Trafford
Borussia Dortmund za ta sake duba yuwuwar zawarcin danwasan gaba na gefe na United, Jadon Sancho, dan Ingila wanda ke zaman aro a Aston Villa, yayin da Tottenham ke kara matsa lamba don sayen mai golan Man City, da Ingila James Trafford.
Fernandez na son tafiya Madrid, Man Utd ta rasa damar samun Anderson
Danwasan tsakiya na Chelsea da Argentina Enzo Fernandez, na shirin miƙa buƙatarsa ta neman tafiya Real Madrid a bazara, yayin da ake ganin Man United ta rasa damar samun Elliot Anderson, na Ingila saboda ya fi son tafiya Man City daga Nottingham Forest.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Abin da muka sani kan 'kisan' Birgediya Janar Oseni Braimah
Ɗaya daga cikin jagororin al'ummar yankin, Zanna Lawan Ajimi ya shaida wa BBC cewa Birgediyar Janar Braimha "na daga cikin sojojin da ƴan ta'addan suka kashe".
Wane ɗauki Amurka za ta iya kai wa ƴan hamayyar Najeriya?
Tun bayan da hukumar zaɓen Najeriya ta INEC ta sanar da cire sunan Sanata David Mark a matsayin shugaban jam'iyyar ADC daga na'urarta, jiga-jigan jam'iyyar suka ɗaura ɗamar yaƙi da abin da suka kira ƙoƙarin danne masu hamayya.
Tarihin yadda bugun fenariti ya samo asali a wasan ƙwallon ƙafa
Tarihi ba zai a taɓa mancewa da Law a matsayin mutum na farko da ya fara ɓarar da bugun fenariti ba, shi kuma McKechnie za zama gola na farko da ya fara buge fenariti.
Mutanen da suka mutu a harin Isra'ila kan Lebanon sun haura 300
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kan yaƙin Iran da kuma muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Alhamis 9 ga watan Afrilun 2026.
Yadda Trump ke son kawo karshen zama ɗan ƙasa ta hanyar haihuwa a Amurka
A tsawon tarihi, Amurka ta kasance tana ba da shaidar zama ɗan ƙasa ga duk wanda aka haifa a ƙasar, amma yaya tsarin yake a sauran ƙasashe?
Yadda Boko Haram ke kai hare-hare a kudancin Borno
Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawan Najeriya ya shaidawa BBC cewa al'ummar yankin na ci gaba da zama cikin fargaba saboda yadda mayaƙan Boko Haram suka dawo da sabon salon kai hare-hare a ƙauykansu.
'Yadda na riƙa wanke kaina da ɗanyen ƙwai domin neman haihuwa'
Kasancewar ta gaji da ganin yadda ake yaɗa labaran ƙarya game da lafiyar mata a shafukan sada zumunta, a yanzu Barbora ta samar da wani shafi domin yaƙi da matsalar.
Amurka ta buƙaci jami'anta su bar Abuja: Me hakan ke nufi?
Amurka ta ce daga cikin dalilan da ta ke ganin ya zama wajibi ƴan ƙasar su bar Najeriya, har da yanayin da asibitocin ƙasar ke ciki, waɗanda ba irin na ƙasashen turai ko Amurka ba ne.
Za mu fice daga yarjejeniyar tsagaita wuta idan Isra'ila ba ta daina kai hari Lebanon ba - Iran
Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 8 ga watan Afrilun 2026.
Ko yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Iran da Amurka za ta ɗore?
Da farko dai za a iya cewa tsagaita wutar wani muhimmin sassauci ne ga fararen hula a yankin Gabas ta Tsakiya waɗanda suka tsinci kansu a tsakiyar yaƙi tun bayan da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da yaƙi kan Iran a ranar 28 ga watan Fabarairu.
Ko jam’iyyun hamayyar Najeriya za su iya shawo kan matsalolinsu gabanin 2027?
''Tilas ne sai jam'iyyun adawa mun haɗa kanmu sannan za mu iya yin nasara kan jam'iyyar APC da ke mulki a Najeriya, domin shi kaɗai ne mafita a wajenmu, idan ba mu dauki wannan mataki ba wankin hula ka iya kai mu dare."
Ko farashin man fetur zai sauka a Najeriya bayan tsagaita wuta a yaƙin Iran?
Farashin man fetur dai ya ƙaru sosai a Najeriya tun bayan da aka fara yaƙin Iran, inda ake hasashen komai zai sauka tunda an dakatar da yaƙin.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.