Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane ne zai samu tikitin takarar shugaban ƙasa a ADC?
A yau ne ake sa ran bayyana sakamakon zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar ADC domin sanin wanda zai samu tikitin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar a zaɓen shekarar 2027, wanda shi ne zai kara da Shugaba Bola Tinubu.
Jam'iyyar dai ta gudanar da zaɓen fitar da gwanin ne a ranar Litinin 25 ga watan Mayu, inda mambobinta daga jihohi 36 na Najeriya da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja suka halarta.
Kwamitin tantance 'yan takarar jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Cross River, Liyel Imoke, ya amince da 'yan takara uku da suka fafata a zaɓen.
'Yan takarar sun haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi da kuma masanin tattalin arziki Mohammed Hayatu-Deen.
Shugabannin jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin David Mark, sun zaɓi gudanar da zaɓen kai tsaye bayan ƙoƙarin cimma matsaya kan ɗan takara guda ɗaya tsakanin manyan masu neman takarar ya ci tura.
Kafin gudanar da zaɓen, jam'iyyar ta buƙaci 'yan takara da wakilai da sauran mambobinta su tabbatar da haɗin kai da bin doka domin tabbatar da zaman lafiya a yayin zaɓen.
A wata sanarwa da kakakin jam'iyyar, Bolaji Abdullahi ya sanya wa hannu, ya bayyana zaɓen fitar da ɗan takarar a matsayin wani muhimmin mataki na dimokuraɗiyya ba kawai ga jam'iyyar ADC ba, har ma ga 'yan Najeriya da ke neman sahihin shugabanci.
Ya ce manufar jam'iyyar ita ce fito da tsayayyar jam'iyya mai haɗin kai da za ta iya bai wa 'yan Najeriya shugabanci nagari kuma abin dogaro, ba tare da ɗaukar zaɓen a matsayin fafatawar masu nasara da masu faɗuwa ba.
Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar na daga cikin masu neman tikitin tsayawa takarar shugaban ƙasa kuma ya yi kira ga jam'iyyar ADC da ta zaɓi ɗan takara mai ƙwarewa da gogewa, wanda zai iya magance matsalolin tattalin arzikin Najeriya da kuma tabarbarewar hukumomi.
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkar yada labarai ya fitar, Atiku ya ce wannan zaɓi ya wuce siyasa kawai, nauyi ne na tarihi.
Ya ce Najeriya na fuskantar matsaloli kamar talauci, rashin tsaro, bashi mai yawa da kuma raunin gwamnati, don haka tana buƙatar shugaba mai kwarewar mulki da fahimtar tattalin arziki.
Atiku ya kuma buƙaci wakilan jam'iyyar su zaɓi cancanta fiye da son rai ko tausayi yayin shirin zaɓen 2027.
Ya ƙara da cewa shi yana da gogewa da ilimin gudanarwa da zai taimaka wajen shugabanci, ba kamar wasu 'yan takara da ke dogaro da magana kawai ba.
A tarihin siyasa, Atiku ya taɓa zama mataimakin shugaban ƙasa daga 1999 zuwa 2007 a zamanin Olusegun Obasanjo, kuma ya sha tsayawa takarar shugaban ƙasa sau da dama ba tare da nasara ba a shekarun 1993, 2007, 2011, 2015, 2019 da 2023.
Ya kuma yi takara a jam'iyyu daban-daban a lokuta daban-daban kafin daga bisani ya koma jam'iyyar ADC a 2025, inda ya nuna sha'awar sake tsayawa takarar shugaban ƙasa.
Rotimi Amaechi
Mutane a Najeriya na ganin tsohon gwamnan Jihar Rivers kuma tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, a matsayin ɗaya daga cikin manyan 'yan takara masu ƙarfi a wannan lokaci, saboda gogewarsa a harkar siyasa.
Amaechi ya taɓa riƙe mukamai da dama, ciki har da kakakin majalisar dokokin Jihar Rivers, sannan kuma ya yi gwamna na jihar. Daga baya ya zama ministan sufuri, inda ya yi fice musamman wajen ayyukan layin dogo da wasu manyan ayyukan sufuri.
Shi ma yana daga cikin waɗanda suka kafa jam'iyyar APC, kuma ya taka muhimmiyar rawa a gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari.
A shekarar 2022, Amaechi ya tsaya takarar shugaban ƙasa a APC, amma ya sha kaye a hannun Bola Tinubu.
Yanzu kuma yana takara a jam'iyyar haɗaka ta ADC, inda yake bayyana kansa a matsayin wanda zai iya kawo canji da dawo da amincewar jama'a ga gwamnati.
Bayan tantance 'yan takara, Amaechi ya ce wakilan jam'iyyar su zabi mutumin da zai iya kayar da shugaban da ke kan mulki, mai gogewa da kuma iya yin aiki mai kyau.
Ya ce: "Ku yi mana hukunci da abin da muka yi. Idan mun yi aiki mai kyau, ku zabi wanda ya fi kowa."
Ya kuma bayyana cewa yana da gogewa sosai, kuma yana ganin zai iya kawo sauyi cikin shekaru huɗu saboda abubuwan da ya cimma a baya.
Mohammed Hayatu-Deen
Wani ɗan takara kuma da ya bayyana aniyarsa ta neman shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar ADC shi ne Mohammed Hayatu-Deen.
Hayatu-Deen ƙwararren masanin tattalin arziki ne, kuma ya taɓa zama babban ma'aikacin banki kuma mai zuba jari, kuma gogagge ne a harkokin kamfanoni. Ya fito daga Jihar Borno, kuma ya shafe fiye da shekara 40 yana aiki a ɓangarorin gwamnati da masu zaman kansu.
A 2015, ya jagoranci kwamitin miƙa mulki kan tattalin arziki ga sabuwar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
A 2023, Mohammed Hayatu-Deen ya sayi fom ɗin takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP, amma ya janye 'yan kwanaki kafin zaɓen fitar da gwani.
Ya ce dalilinsa shi ne tsarin zaɓen bai yi daidai ba, kuma bai gamsu da yadda aka yi amfani da kuɗi wajen siyasar ba,
Jam'iyyar ADC ta ce Hayatu-Deen yana da gogewa mai zurfi a fannin tattalin arziki da gyaran harkokin kuɗi, da kuma ci gaban ƙasa.