BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
KAI TSAYE, Donald Trump ya ce yana gab da samun galaba kan Iran
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman bayanai dangane da yaƙin Iran da ma sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na 21/04/2026
Yadda tikitin wasan ƙarshe na gasar cin Kofin Duniya na dala 11,000 ke jan hankali
Abu ne mai wuya a gano abin da ya janyo tikitin ya yi tsadar gaske saboda Fifa ba ta fitar da yadda take tsara farashin tikiti ba.
Dalilai huɗu da suka sa tattaunawar Iran da Amurka ke cikin ƙila-wa-ƙala
Makomar tattaunawar Iran da Amurka ta shiga cikin rashin tabbas yayin da lokacin da aka ɗebe na tsagaita wuta ke daf da karewa.
Yadda magoya bayan Obi da Kwankwaso suka kafa ƙungiya don samun tikitin ADC
Magoya bayan tsoffin yan takarar shugaban kasa a Najeriya Peter Obi, da kuma Rabiu Musa Kwankwaso sun kafa wata kungiya mai suna Obi–Kwankwaso (OK Movement) da ta soma tattaunawa domin ganin jam'iyyar ADC ta tsayar da su takarar shugaban kasa da mataimaki a zaben 2027 da ke tafe.
Wane tasiri toshe hanyoyin ruwa ke yi a yaƙin Iran?
Amurka da Iran sun yi amfani da batun toshe hanyoyin ruwa a yaƙin da ake yi yanzu. Don haka me tarihi ya nuna kan tasirin wannan mataki?
Me komawar Malam Shekarau APC ke nufi a siyasar Kano?
A ƙarshen makon nan ne tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya fice daga jam'iyyar hamayya ta PDP inda ya koma jam'iyya mai mulki ta APC.
Diomande zai maye gurbin Salah a Liverpool,Newcastle za ta sayar da Gordon
Dan wasan RB Leipzig da Ivory Coast Yan Diomande, mai shekara 19, shi ne wanda Liverpool ta ke son ta dauka domin maye gurbin dan wasan Masar Mohamed Salah
Abin da Kotun Ƙoli ta ce kan rikicin Masarautar Kano
A wani zaman da ta yi a Abuja, kotun ta ƙoli ta ɗage zaman sauraron shari'ar zuwa ranar 19 ga watan Afrilun 2027, wato kimanin shekara ɗaya daga yanzu.
Dole a samar da tsaro a Najeriya - Hafsan hafsoshi
Wannan shafi na kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa dangane da yaƙin Iran da kuma sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na 20/04/2026
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Yamma, 19:29, 21 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Rana, 13:59, 21 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 21 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 21 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Wasanni
KAI TSAYE, Casemiro: Man United na cikin manyan ƙungiyoyi uku a duniya
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga ranar Lahadi 19 zuwa Juma'a 24 ga watan Afrilun 2026.
Hanyoyi uku da suka rage wa Arsenal na lashe kofin Premier
Rashin nasarar da ƙungiyar ta yi da ci 2-1 ya sake jefa ta cikin babbar barazanar gaza lashe Kofin Premier da ta shafe fiye da shekara 20 tana ƙishirwarsa.
Man United da Real Madrid na zawarcin Emery, Arsenal da Chelsea na son Bergvall
Hankalin Manchester United da Real Madrid ya koma kan Kocin Aston Villa Unai Emery, ko da yake Villa na da kwarin gwiwa a kansa
Madrid na son dawo da Mourinho, Onyeka zai koma Conventry
Real Madrid na tunanin nada tsohon kocinta Jose Mourinho wanda ke jagorantar Benfica
Hanyoyin daidaita lokacin motsa jiki domin samun sakamako mafi kyau
Masu tashi da wuri, wato yan safe kenan ya kamata su motsa jiki da safe domin samun cikakken amfani, yayin da wadanda suke yan dare ne ya fi dacewa su motsa jiki da yamma, in ji masu bincike.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kashe ƙwarƙwatar ido
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Da me Turkiyya za ta taimaka wa Najeriya ta fuskar tsaro?
Yarjejeniyar - wadda aka ƙulla tsakanin ministan tsaron Najeriya da takwaransa na Turkiyya - ta ƙunshi samar da babban sansanin bayar da horo ga dakarun Najeriya, kamar yadda shalkwatar tsaron Najeriya ta bayyana.
Yaran da aka haifa kusa da sansanin sojin Birtaniya a Kenya sun gano gaskiya kan mahaifansu
Wani lauya a Birtaniya James Netto da kuma wani Kelvin Kubai a Kenya, sun ce akwai kusan yara 100 da aka haifa kusa da sansanin sojin Birtaniya a Kenya.
Mece ce manhajar Claude Mythos kuma wanne haɗari ke tattare da ita?
Manhajar Mythos za ta iya fin ɗan adam ƙoƙari kuma tana da kwarewa wajen tsaron intanet sai dai wannan ikirari da kamfanin Anthopic ya yi, ya haifar da tsoro a zukatan masu amfani da manhajojin kuɗi a duniya
Son yin takara ne a gaban 'yan ADC ba Najeriya ba - Shekarau
Tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau, ya ce son yin takara ne a gaban jiga-jigan da ke jagorantar tafiyar ADC, ba wai bukatar ciyar da kasar gaba ba.
Har yanzu tsugune ba ta ƙare ba a yaƙin Iran - Netanyahu
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, 19/04/2026
Yaushe duniya za ta fuskanci sauyin yanayi na 'Super El Niño'?
Masana kimiyar sauyin yanayi sun yi gargarɗin cewa ka da a ruɗu da hasashen sauyin yanayi a watan Maris da Afrilu.
Wane ne fir'aunan da ya yi zamani da annabi Musa?
Littattafan addini na baya su ma ba su ambato sunan wannan "Fir'aunan" ba, wanda ya mulki Misra kuma ya yi rayuwa da Annabi Musa.
Yadda zargin sakaci ke janyo salwantar rayuka a asibitin Jami'ar Maiduguri
Jama'a a Najeriya na ci gaba da korafi kan zargin sakaci da aiki, da rashin kyakkyawar kulawar da ta dace ga majinyata a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri a jihar Barno, al'amarin da ake zargin yana jefa majinyatan cikin mawuyacin hali, har ma da kai wasunsu ga rasa rayukansu.
Wurare 5 da suke nuna tarihin cinikin bayi a Afirka
Tsananin azabar da aka sha lokacin cinikin bayi, musamman a yankunan baƙar fata na ƙara tabbatar da yadda bauta ta taka muhimmiyar rawa a tarihin nahiyar Afirka.
Wankan safe ko na dare: Wanne ya fi amfani?
Wanke muhimman wurare a jiki tare da yin wanka na wasu kwanaki a mako zai haifarwa da mutum rayuwa cikin ingantacciyar lafiya
Ba za mu buɗe Hormuz ba sai Amurka ta buɗe tashar ruwanmu - Iran
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Asabar 18/04/2026
Da gaske hasken waya na haifar da matsala ga bacci?
Yadda rage haske da maraice ya ke taimakawa wajen samun bacci cikin sauƙi
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.

































































