'Yansandan Najeriya sun gano wurin ƙera bindigogin farauta a Yobe
Rundunar ƴansandan Najeriya reshen Jihar Yobe ta sanar da gano wani haramtaccen wurin ƙera makamai a garin Potiskum tare da kama mutane bakwai da ake zargi da hannu a aikin.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta bayyana nasarar a matsayin ɗaya daga cikin manyan matakan da ta samu wajen yaƙi da laifuffuka a jihar.
Kakakin rundunar a jihar, SP Dungus Abdulkarim, ya ce kamen ya biyo bayan sabbin tsare-tsaren da Kwamishinan ƴansandan jihar ya ƙaddamar domin daƙile ayyukan ta'addanci da sauran laifuffuka a faɗin Yobe.
A cewarsa, a ranar 2 ga Yunin 2026 da misalin ƙarfe shida na yamma, rundunar ta samu sahihan bayanan sirri cewa wasu maƙera na ƙera bindigogin katako da sauran makamai ba bisa ƙa'ida ba.
Daga nan ne rundunar yankin Potiskum tare da haɗin gwiwar hedikwatar 'yansanda ta gudanar da samame a wani wajen maƙera da ke Tasha Adua kan titin Danchuwa a Potiskum.
SP Abdulkarim ya ce a yayin samamen an kama mutane bakwai tare da ƙwace wasu kayayyaki da suka haɗa da bindigogi da aka ƙera da dai sauransu.
Ya ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi kan waɗanda ake zargin domin gano abokan hulɗarsu da masu sayen makaman da kuma manufar amfani da su.