Taron G7: 'Rikicin Libya na kara tsananta matsalar tsaro a yankin Sahel'

Akwai sojojin kasashen duniya da ke yaki da ta'addanci a yankin Sahel

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Shugaban Burkina Faso Marc Kabore ya bukaci shugabannin kasashen duniya su mayar da hankali wajen kawo karshen rikicin da ake fama da shi a Libya kafin a iya kakkabe ta'addancin da ke bazuwa a fadin Sahel.

Shugaban ya fadi hakan ne a wani jawabi da ya gabatar a taron kolin manyan kasashe bakwai masu ci gaban masana'antu a Biarritz tare da takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron.

Mista Kaboré ya yi kira da a samar da isassun kudade ga rundunar yaki da ta'addanci da ke aiki a yankin Sahel mai lakabin G- five.

Shi dai shugaba Kabore, wanda a makon jiya aka kashe sojojin kasarsa 24 tare da jikkata wasu guda 7 a wani harin 'yan tayar da kayar baya, ya bayyana ta'addanci amatsayin wata masifa da ke bazuwa a Afirka.

Ya ce "Masifa ce da ke yaduwa, kuma mun yi kiyasin cewa sai dukkanin abokan kawance sun hadu domin lalubo mafita ga matsalar tsaro a Libya."

Ya kara da cewa sai kasashen duniya sun zuba jari wajen samar da ayyukan raya kasa da ayyukan soja, kafin zaman lafiya ya tabbata a yakin Sahel.

A nata jawabin a wurin taron na G7, shugabar Jamus Angela Merkel ta ce al'amura na ci gaba da tabarbarewa a Sahel.

Ta ce abin da ke faruwa a Afirka abin damuwa ne, saboda haka akwai bukatar al'ummomin kasashen duniya su hanzarta tashi tsaye domin ganin kungiyoyin 'yan ta'adda ba su samu wurin zama ba a can.

Ta ce "A yakin da muke yi, ba mu kai gabar da za mu ce sha'anin tsaro ya inganata ba".