Me ya sa majalisar dattawa ke neman zama matattarar tsoffin gwamnoni?

Wasu gwamnonin Najeriya da ke son tafiya majalisar dattawa

Asalin hoton, Multiple

    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Jam'iyyun siyasa a Najeriya na ci gaba da gudanar da zaɓukan fitar da gwanin takarar majalisar dattawan ƙasar a zaɓen 2027 da ke tafe.

Tuni gwamnoni masu ci akalla takwas suka samu tikitin takarar majalisar a zaɓen 2027 da ke tafe.

Majalisar dattawan ɗaya ce daga cikin majalisun dokokin Najeriya mai tasiri a siyasar kasar.

Zauren majalisar na ƙunshe da mambobi 109, da ake zaɓowa uku daga kowace jiha, sai birnin Abuja mai guda ɗaya.

Manyan ayyukan majalisar sun haɗa da samar da dokoki da amincewa da mutanen da shugaban ƙasa ke son naɗawa manyan muƙaman gwamnatinsa ciki har da ministoci.

Kamar yadda sunanta ya nuna majalisar na ƙunshe da mutane masu shekaru da ƙwarewa, musamman la'akari da irin tasirin majalisar.

Majalisar dattawan na ƙunshe da tsoffin gwamnonin da suka gama mulkin jihohinsu da kuma tsoffin ƴanmajalisar wakilai.

Tsoffin gwamnoni nawa ne suka shiga majalisar dattawa?

Tun shekarar 2007 - lokacin da gwamnonin zangon farko na jamhuriya ta hudu da aka zaba a 1999 suka ƙare wa'adi biyu da suka faro a 1999 - zuwa yanzu an samu tsoffin gwamnoni fiye da 40 da suka shiga zauren majalisar dattawan ƙasar.

Majalisa ta tara da aka yi tsakanin 2019 zuwa 2023 ce ta fi ƙunsar tsoffin gwamnoni a cikinta.

Majalisa ta 10

Shugaban majalisar dattawan Najeriya

Asalin hoton, Sen. Godswill Akpabio/X

Bayanan hoto, Godswill Akpabio ya yi gwamnan Akwa Ibom wa'adi biyu kafin ya shigar majalisar dattawa, wanda a yanzu yake jagoranta.

Majalisa ta 10 da ke gudana a yanzu, na ƙunshe da tsoffin gwamnoni 13, da suka haɗa da:

  • Adamu Aliero (Kebbi)
  • Aminu Tambuwal (Sokoto)
  • Aliyu Wammako (Sokoto)
  • Abdulaziz Yari (Zamfara)
  • Godswill Akpabio (Shugaban majalisar, Akwa Ibom)
  • Seriake Dickson (Bayelsa)
  • Adams Oshiomole (Edo)
  • Sani Bello (Neja)
  • Simon Lalong
  • Ibrahim Hassan Dankwambo (Gombe)
  • Danjuma Goje (Gombe)
  • Orji Uzor Kalu (Abia)
  • Gbenga Daniel (Delta)

Majalisa ta 9

Ibrahim Gaidam

Asalin hoton, Ibrahim Gaidam

Bayanan hoto, Ibrahim Gaidam ya yi wa'adi biyu a matsayin gwamnan Yobe kafin ya shiga majalisa ta tara

Majalisa ta tara da aka yi tsakanin 2019 zuwa 2023 ce ta fi kunsar tsoffin gwamnoni, inda take da 16, da suka hada da:

  • Orji Uzor Kalu (Abia)
  • Theodore Orji (Abia)
  • Kashim Shettima (Borno)
  • Sam Egwu (Ebonyi)
  • Chimaroke Nnamani (Enugu)
  • Danjuma Goje (Gombe)
  • Rochas Okorocha (Imo)
  • Ibrahim Shekarau (Kano)
  • Kabiru Gaya (Kano State)
  • Adamu Aliero (Kebbi)
  • Tanko Al-Makura (Nasarawa)
  • Abdullahi Adamu (Nasarawa)
  • Ibikunle Amosun (Ogun)
  • Aliyu Wamakko (Sokoto)
  • Ibrahim Gaidam (Yobe)
  • Gabriel Suswam (Benue)

Majalisa ta 8

Bukola Saraki

Asalin hoton, Facebook/Nigerian Senate

Bayanan hoto, Bukola Saraki ya mulki jihar Kwara tsawon wa'adi biyu kafin ya zama shugaban majalisar dattawa

Majalisar ta takwas - wadda ta wanzu tsakanin 2015 zuwa 2019 - na ƙunshe da tsoffin gwamnoni 10 da suka haɗa da:

  • Bukola Saraki (Kwara State – shugaban majalisar ta 9)
  • Godswill Akpabio (Akwa Ibom)
  • George Akume (Benue)
  • Ahmed Sani Yerima (Zamfara)
  • Rabiu Musa Kwankwaso (Kano)
  • Jonah Jang (Plateau)
  • Joshua Dariye (Plateau)
  • Shaaba Lafiagi (Kwara)
  • Isiaka Adeleke (Osun)
  • Bukar Abba Ibrahim (Yobe)

Majalisa ta 7 da ta 6

Makarfi

Asalin hoton, Facebook/Nigerian Senate

Waɗannan ne lokacin da ba a samu tsoffin gwamnoni da yawa a zauren majalisar ba.

A duka majalisun biyu tsoffin gwamnoni huɗu ne kawai suka shige su da suka haɗar da:

  • Ahmed Makarfi (Kaduna)
  • Saminu Turaki (Jigawa)
  • Abdullahi Adamu (Nasarawa State)
  • Chris Ngige (Anambra State)

Gwamnoni masu ci da suka samu tikitin 2027

Ahmadu Umaru Fintiri

Asalin hoton, Ahmadu Umaru Fintiri/FB

Bayanan hoto, Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri na cikin wadanda ke son tafiyar majalisa ta 11 a 2027

Ya zuwa yanzu da jam'iyyu suka fara zaɓukan fitar da gwani, jam'iyyar APC mai mulki ta bai wa gwamnoni bakwai tikitin tarakar majalisar dattawan waɗanda suka haɗa da.

  • Dapo Abiodun: (Ogun)
  • Hope Uzodinma: (Imo)
  • Ahmadu Fintiri: (Adamawa)
  • Abdullahi Sule: (Nasarawa)
  • AbdulRahman AbdulRazaq: (Kwara)
  • Muhammad Inuwa Yahaya: (Gombe)
  • Mai Mala Buni: (Yobe)

Sai kuma gwamnan Bauchi, Bala Mohammed da ya bayyana sha'awar tsayawa takarar a sabuwar jam'iyyarsa ta APM.

Muhammad Inuwa Yahaya

Asalin hoton, Muhammad Inuwa Yahaya

Bayanan hoto, Yayin da yake dab da kammala wa'adin mulkinsa na biyu, gwamnan Gombe ya samu tikitin takarar 2027

Me ya sa tsoffin gwamnonin ke tafiya majalisar dattawan?

Farfesa Abubakar Umar Kari, malami a Jami'ar Abuja, kuma mai sharhi kan al'amuran siyasa a Najeriya ya ce dalilin kawai shi ne gwamnonin ba sa son barin fagen siyasa.

''Ba sa so a ce sun rasa madafun iko ko kuma a ce sun faɗi ƙasa a siyasance, shi ne ma ya sa ya zama kamar wata al'ada a wannan jamhuriya cewa idan gwamnan ya gama wa'adinsa biyu sai ya tafi majalisar dattawa'', in ji shi.

Sai dai masanin siyasar ya ce ba lallai ne hakan ya taimaki tsarin dimokraɗiyya ba.

''Hasalima a wasu lokutan hakan ka iya zama babakere, domin kuwa za ka samu waɗannan gwamnoni na karɓar fanshonsu na tsoffin gwamna, kuma a lokaci guda suna karɓar albashi da alfarmar majalisar dattawa'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Shin suna taka rawar gani a majalisar?

Kasancewar tsoffin gwamnonin na da gogewar siyasa wasu ke ganin zuwansu majalisar dattawan zai taimaka wajen inganta aikin majalisar.

Amma Farfesa Kari ya ce babu wata gagarumar rawa da tsoffin gwamnonin ke takawa a majalisar, duk kuwa da ƙwarewar da ake ganin suna da ita a siyasance.

''Da yawansu ɗumama kujera kawai suke yi da ma kawo cikas ga ayyukan majalisar'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa ai dama ba lallai ba ne don kawai mutum ya yi gwamna a ce kuma ya iya taka wata rawa a majalisa, saboda bambancin muƙaman biyu.

''Muƙamin gwamna, matsayi ne na zartaswa, kai ne mai wuƙa da nama a jiha, da tasrifin kasafin kuɗin jiharka, yayin da kujerar ɗan majalisa dattawan ta ƙunshi yin dokoki da wakilci da sanya idanu kan harkokin gwamnati'', in masanin siyasar.