Wane ne Alexx Ekubo, jarumin Nollywood mai jin Hausa da ya rasu?

Asalin hoton, Alexx Ekubo/ Facebook
Fitaccen jarumin masana'antar shirya fina-finai ta Nollywood, Alexx Ekubo, wanda ya iya harshen Hausa sosai kuma ya yi karatun sakandare a makarantar Federal Government College Daura da ke Jihar Katsina, ya rasu yana da shekara 40 bayan ya shafe lokaci yana fama da cutar daji.
Marigayin na daga cikin shahararrun taurarin masana'antar Nollywood inda ya yi suna wajen fitowa a fina-finai da harkar kwaikwayo da kuma tallace-tallace.
Rahotanni sun bayyana cewa Alexx Ekubo ya rasu ne a wani asibiti ranar Talata. Har yanzu iyalansa ko masu kula da harkokinsa da kuma ƙungiyar masu shirya fina-finai ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba.
Tarihin Alexx Ekubo

Asalin hoton, Alexe Ekubo/Facebook
An haifi fitaccen jarumin Alexx Ekubo a ranar 10 ga watan Afrilu, 1986 a birnin Port Harcourt da ke Jihar Rivers, yayin da asalinsa ya fito ne daga Arochukwu a Jihar Abia.
An san shi da tsayi da kwarjini da kuma irin yadda yake jan hankali a fina-finai.
Marigayin ya iya magana da harshen Hausa sosai da Turanci da kuma Igbo.
Ya yi karatun sakandare a makarantar Federal Government College Daura da ke jihar Katsina daga baya ya karanci shari'a a jami'ar Calabar sannan ya kuma samu digiri a fannin sadarwa daga kwalejin kimiyya da fasaha ta Calabar.
Alexx Ekubo ya fara samun karɓuwa a Najeriya ne a shekarar 2010 bayan ya zo na biyu a gasar Mr Nigeria.
Wannan ne ya buɗe masa hanya zuwa harkar kwaikwayo da tallan kaya kafin daga baya ya zama ɗaya daga cikin fitattun jaruman Nollywood.
Fina-finan da Alexx ya fito

Asalin hoton, Alexx/Facebook
Ko da yake fim dinsa na farko mai muhimmanci shi ne Ladies Men, Alexx ya taka rawa a fina-finai sama da 116 a rayuwarsa.
Fim dinsa na baya-bayan nan shi ne Adanne wanda aka saki a watan Fabrairun wannan shekarar ta 2026.
Ya fito a manyan fina-finai da dama da suka hada:
- Lagos Cougars
- Weekend Getaway
- In the Cupboard
- Dream Walker
- Hire a Woman
- Sugar Rush
- Merry Men
- The Real Yoruba Demons
- Fate of Alakada
Alex ya samu lambobin yabo 9
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A tsawon lokaci ya yi suna musamman wajen taka rawar soyayya a fina-finan zamani na Najeriya.
Alexx Ekubo ya lashe kyautar gwarzon jarumi a gasar Best of Nollywood Awards ta shekarar 2013 saboda rawar da ya taka a fim din Weekend Getaway.
A shekarar 2018 kuma ya samu lambar yabo ta musamman daga matar shugaban ƙasa ta Najeriya saboda gudunmawar da yake bayarwa wajen bunƙasa masana'antar nishaɗi ta Najeriya.
A shekarar 2020 an saka shi cikin jerin fitattun mutane bakar fata masu tasiri a duniya yan ƙasa da shekara 40 tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya.
Haka kuma a shekarar 2021 jami'ar Institut Supérieur de Communication et de Gestion ta ba shi digirin girmamawa a fannin fasaha da al'adu.
Ya kuma samu lambar yabo ta ƙasa saboda ayyukan taimakon al'umma da ya riƙa yi.
Marigayin jarumin ya samu lambobin yabo guda tara a tsawon aikinsa.
Baya ga harkar fim, Alexx Ekubo ya kasance yana shiga ayyukan jin ƙai da taimakon al'umma, lamarin da ya ƙara ɗaga martabarsa a Najeriya da ma duniya baki daya.
Alhini daga abokan aikin Alexx

Asalin hoton, Alexe/Facebook
Tuni abokan aikinsa a masana'antar Nollywood suka fara bayyana alhini da jimamin rasuwarsa.
Fitacciyar jaruma kuma mai shirya fina-finai, Funke Akindele, ta wallafa a shafinta na Instagram tana cewa, "Ka huta lafiya Alex."
Alexx Ekubo da Funke Akindele sun taba fitowa tare a fim din Omo Ghetto: The Saga wanda aka saki a shekarar 2020.
Rasuwar tasa na zuwa ne bayan wasu mutane a masana'antar Nollywood sun riƙa wallafa sakonni masu rikitarwa dangane da rayuwar jarumin mai shekaru 40.
Jarumin, wanda ya fara haskawa a masana'antar fim tun shekarun 2010, ya daɗe bai wallafa komai a shafukan sada zumunta ba, duk da cewa yana ci gaba da harkar fim.
Sauran fitattun jaruman da suka nuna jimaminsu sun hada da Rita Dominic da Bolanle Ninalowo.
Rahotanni sun nuna cewa tun watan Disambar 2024 ne Alexx Ekubo ya yi wallafarsa ta ƙarshe a shafukan sada zumunta, lamarin da ya haddasa damuwa tsakanin masoyansa.
Alexx na da mabiya miliyan 4.2 a shafinsa na Instagram, sai kuma miliyan 2.7 a Facebook, inda yake da fiye da dubu 140 a X sannan kuma yana da fiye da 500 a Tiktok.






