AC Milan na son Glasner a matsayin kocinta, Newcastle na zawarcin Ezzalzouli

Oliver Glasner

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Oliver Glasner
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Tsohon kocin Crystal Palace Oliver Glasner na shirin tattaunawa da AC Milan kan mukamin kocin kungiyar bayan sallamar da ta yi wa Massimiliano Allegri.(Mail), external

Bayern Munich na zawarcin dan wasan Bournemouth da Faransa Junior Kroupi, mai shekara 19, a matsayin wanda zai maye gurbin dan wasan Colombia Luis Diaz a lokacin wasa . (Absolut Bayern via Merkur - in German), external

Liverpool da Inter Milan suna tattaunawa kan cinikin dan wasan Ingila Curtis Jones, mai shekara 25, amma Liverpool ta fi son a ba ta kudi fiye da yuro miliyan domin ta sayar da dan wasan.(Fabrizio Romano)

Dan wasan Brazil da Galatasaray, Gabriel Sara mai shekara 26 ya maida martani mai kyau ga Aston villa da ke zawarcinsa. (Sabah - in Turkish), external

Chelsea na sha'awar dan wasa mai kai hari Mikkel Bro Hansen, mai shekara 17 wanda kwanragarinsa a Bodo/Glimt zai zo karshe a 2027, sai dai Newcastle da Manchester City sun sa ido kan matashin dan kasar Denmark. (Caught Offside), external

Sporting na tunanin bada aron dan wasan Girka da Everton Georgios Vagiannidis mai shekara 24 (A Bola - in Portuguese), external

Chelsea ta yanke shawarar dakatar da tayin da za ta yi wa dan wasan Liverpool wanda zai bar kungiyar, Ibrahima Konate mai shekara 27 kuma wakilan dan kasar Faransa na tattaunawa da wakilan Real Madrid da Bayern Munich.(Teamtalk), external

Juventus na bibiyar tsohon golan Manchester United da Sfaniya,David de Gea, mai shekara 35 wanda shi ne golan Florentina. Goal), external

Preston North End ta yanke shawarar siyan dan wasan Tottenham Alfie Devine a tattaunawar ba da shi aro kuma a shirye suke su kafa tarihi a musayyar da suke son su yi kan dan wasan Ingila mai shekara 21. (Lancashire Post), external

Dan wasan Moroko da Real Betis Abde Ezzalzouli mai shekara 24, ya bayyana a matsayin wanda watakila zai maye gurbin tsohon dan wasan Newscastle AnthonyGordon inda Tottenham da Aston Villa ke zawarcinsa. (Sport - in Spanish)