Mutumin da ya sayi tikitin APC don ƙalubalantar Tinubu

Stanley da Tinubu

Asalin hoton, Multiple

Lokacin karatu: Minti 2

Yayin da mafi yawan jagororin jam'iyyar APC, mai mulkin Najeriya suka nuna amincewarsu ga Shugaba Tinubu a matsayin ɗan takara ɗaya tilo da zai tsaya wa jam'iyyar takarar 2027, an samu wani mutum da ya sayi fom ɗin takarar shugaban ƙasar.

Mutumin mai suna Stanley Osifo na shirin ƙalubalantar Shugaba Tinubu a zaɓen fitar da gwanin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar a zaɓe mai zuwa.

Bayanai na nuna cewa Mista Osifo ya sayi form ɗin takarar shugaban ƙasa kan kuɗi naira miliyan 100 a shalkwatar jam'iyyar, kuma tuni ya cika tare da mayar da form ɗin.

A nasa ɓangare Shugaba Tinubu, ya mayar da form ɗin da ya cika domin tsayawa takarar, wanda mataimakinsa Kashim Shettima ya mayar da shi ranar Alhamis a madadinsa.

Cikin wata sanarwa da Shettiman ya fitar ya yi kira ga masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da suka haɗa da gwamnoni da ƴanmajalisar dokoki su goya wa shugaban baya a ƙudirin nasa.

Kawo yanzu dai Mista Osifo ne ɗan takara ɗaya tilo a APC da ya ƙudiri aniyar ƙalubalantar Tinubu a zaɓen fitar da gwanin jam'iyyar.

Wane ne Stanley Osifo?

Osifo Stanley

Asalin hoton, Stanley Osifo/FB

Stanley Osifo haifaffen garin Benin ne daga jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya.

Ɗan siyasar mai shekara 50, ya taɓa tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2019.

Yayin da yake jawabi ga taron manema labarai a Abuja, ranar Talata, mista Osifo ya ayyana kansa a matsayin ɗan kishin ƙasa, wanda ke da muradin mayar da Najeriya ɗaya daga cikin mafiya ci gaban tattalin arziki.

A 2019 ne, Stanley ya koma jam'iyyar APC, kwanaki kafin zaɓen shugaban ƙasa.

Osifo ya ce abubuwan da zai mayar da hankali a kansu sun haɗa da tattalin arziki da tsaro da kiwon lafiya da samar da ruwan sha da ci gaban yankunan ƙasar daban-daban.

Masalaha ko zaɓen fitar da gwani?

Jam'iyyar APC dai galibi kan yi mafani da hanyar masalaha wajen fitar da ƴantakarar.

To sai dai Mallam Bala Ibrahim Daraktan yaɗa labaran sakatariyar jam'iyyar na ƙasa ya ce a wannan karo za a yi amfani da zaɓen ƴantinƙe ne domin fitar da ɗan takatar shugaban ƙasar.

Yayin hirarsa da BBC, Mallam Bala ya ce ''tun da ya sayi fom ya cika ya kuma dawo da shi, ka ga ya nuna yana son ya tsaya takara kenan''.

Jam'iyyar dai ta saka ranar 23 ga watan Mayu, domin gudanar da zaɓen fitar da gwani na ƴantakarar shugaban ƙasar.

Su wane ne za su yi zaɓen fitar da gwanin?

Mallam Bala Ibrahim ya ce za a gudanar da zaɓen fitar da gwanin takarar shugaban ƙasar a Abuja, babban birnin ƙasar.

Sabuwar dokar zaɓen ƙasar dai ta yi tanadin cewa masu riƙe da katin jam'iyya na da damar kaɗa ƙuri'arsu a zaɓen fitar da gwanin.

To amma Bala Ibrahim ya ce akwai wasu keɓantattun mutane da dokar jam'iyyar APC ta amince su shiga zaɓen ƴartinƙen domin fitar da gwanin.

"Akwai wasu abubuwa da za mu yi la'akari da su wajen fayyace waɗanda za su shiga zaɓen na fitar da gwanin takarar shugaban ƙasa'', in ji shi.

''Ƴan jam'iyya ne cikakku masu katin jam'iyya, waɗanda ke biyan haƙƙoƙin jam'iyya, da sauran sharuɗɗan da aka gindaya, ba wai duk wanda ya mallaki katin jam'iyya kawai ba'', kamar yadda Mallam Bala Ibrahim ya bayyana.

Ya ƙara da cewa ''magoya bayan kowa za su fito su jeru a bayansa, domin ganin wanda nasa suka fi yawa domin samun nasara'', in ji shi.