Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa Afrika ke neman a samar da sabuwar taswira a duniya?
Afrika ita ce nahiya ta biyu mafi girma a duniya, inda take da faɗin ƙasa da ya kai kilomita miliyan 30.37.
Duk da haka, a kan taswirar Mercator, an bayyana ta daidai da girman Greenland, yankin da Trump ke so kuma wanda bai wuce kilomita miliyan 2.5 ba.
Giɓin da aka samu na asalin girman wannan nahiya yana da nakasu na yadda wasu za su kalli Afrika.
Wannan shi ne ra'ayin ƙungiyar Tarayyar Afrika, wadda ke da'awar samar da sabon taswira, da zai bayyana ainihin girman nahiyar kan taswira.
A yanzu, Togo wadda AU ta ɗora wa alhakin mara wa wannan da'awar, za ta buƙaci ƙasashe mambobin Majalisar Ɗinkin Duniya da su yi amfani da taswirar da ke bayyana gaskiyar girman nahiyar.
Togo na jagorantar da'awar
Togo za ta buƙaci dukkan ƙasashe mambobin Majalisar Ɗinkin Duniya da su riƙa amfani da taswirar da ke bayyana ainihin yadda Afrika take sannan su yi watsi da alkaluman ta Mercator, kamar yadda ministan harkokin wajen ƙasar ya faɗa wa Reueters.
"Faɗin nahiyar Afrika da muke ganin a kan taswirar duniya bai yi daidai ba," in ji Robert Dussey yayin tattaunawa da Reuters ranar Litinin.
A farkon wannan shekara, Tarayyar Afirka ta zartas da wani kuduri da nufin inganta asalin girman nahiyar tare da karfafa gwiwar ƙasashe mambobinta 55 da su yi watsi da hasashen Mercator.
"Kalubalen shi ne samun kudurin da babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya zai amince da shi don tabbatar da wannan taswira," kamar yadda mista Dussey ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters. Ya kara da cewa, "Ƙasashen Afirka sun riga sun amince da wannan yunkuri."
Tarayyar Afrika ta buƙaci Togo ranar 7 ga Afrilu da ta gabatar da daftari gaban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya na gaba don samun damar watsi da hasashen taswirar Mercator.
Bayanai mara gaskiya kan Afrika a taswira
Masu suka sun kalubalanci cewa alkaluman Mercator, wanda ya saka faɗin Greenland yin daidai da na Afrika wanda kuma a ainihi Afrika ta yi girman yankin har sau 14, ya sake nuna yadda aka ware Afrika duk da irin girman da take da shi da kuma yawan al'umma, kuma hakan yana tasiri kan irin tattaunawa da ake yi a kafafen yaɗa labarai da fannin ilimi da kuma na siyasa.
Don gyara wannan kuskure na rashin saka ainihin bayanan Afrika a taswira, AU ta shiga sahun masu kamfe na "Gyara Taswira" wanda ke son gwamnatoci da kuma ƙungiyoyi su kawo karshen amfani da bayanan Mercator.
Wannan shiri, wanda ƙungiyoyin Africa No Filter da Speak Up Africa ke jagoratanta, na kiran a koma amfani da bayanan 2018, waɗanda suka bayyana ainihin faɗin yankin yadda yake.
"Ba wai saka Afrika a taswira bane, muna son tabbatar da cewa duniya ta kalli nahiyar yanda take a ainihi," in ji Moky Makura darektan ƙungiyar Africa No Filter.
Abin da ba za a lamunta ba
Watakila bayanai da ba gaskiya ba kan Afrika sun yi tasiri a kan tunaninmu kuma sun rage mahimmancin nahiyar Afirka a duniya. Moky Makura ya ce "Wannan shi ne lokaci na labaran ƙarya mafi tsawo a duniya, kuma dole ne a dakatar da shi," in ji Moky Makura.
Ga waɗanda ke son a koma amfani da sabon taswira, sun ce labaran ƙarya a kan Afrika sun yi tasiri mara kyau kan fannin ilimi, yadda ake tunani, siyasa da kuma ƙimar nahiyar da yanda ake tattaunawa a kanta a kafafen yaɗa labarai.
Fara Ndiaye, wadda tana ɗaya daga cikin mutanen da suka assasa ƙungiyar Speak Up Africa, ya ce bayanan Afrika da taswirar Mercator ta gabatar ba su fito da asalin Afrika ba da kuma alfaharin ƴan nahiyar, musamman yaran da za a fuskanta da shi nan gaba yayin da suke shiga makaranta.
"Muna aiki tukuru wajen samar da tsarin karatu da zai bayyana yanda asalin faɗin nahiyar yake a faɗin makarantu a Afrika," in ji Ms Ndiaye, inda ta ce tana fatan hukumomin duniya su ma za su koma amfani da asalin bayanan, ciki har da waɗanda ke zaune a Afrika.
Mercator - taswirar da ba za a so tunawa da ita ba
Taswirar wadda mai zane Gerardus Mercator ya kirkiro don wasu, ya gabatar da bayanai da ba na gaskiya ba kan asalin girman nahiyoyi, inda ya faɗaɗa wasu yankuna, kamar Arewacin Amurka da Greenland, yayin da ya rage faɗin Afrika da Kudancin Amurka.
Har yanzu ana amfani da bayanan taswirar, musamman ma makarantu da kamfanonin fasaha a faɗin duniya.
Ƙungiyar Tarayyar Afrika yanzu ta shiga sahun kamfe ɗin waɗanda ke son a daina amfani da taswirar, musamman ma gwamnatoci da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, inda ake son su koma amfani da wanda ya bayyana ainihin yadda girman nahiyar yake.