KAI TSAYE, Premier League: West Ham ta faɗa Championship, Tottenham ta tsallake rijiya da baya, Sunderland zuwa Europa, Arsenal ta dauki Premier

Wannan shafi ne da ke kawo muku wainar da ake toyawa a ranar ƙarshe ta gasar Premier Ingila

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Buhari Fagge

  1. Hawaye na ci gaba da bin kumatun Salah

    Mo Salah ya kasa daina zubar da hawaye lokacin da yake bankwana da masoyansa da na ƙungiyarsa.

    Liverpool da magoya bayanta ba za su taba mantawa da Salah ba

    s

    Asalin hoton, Getty Images

  2. Kaka mai ɗan kare wuya ga Tottenham, Tottenham 1-0 Everton

    Samun nutsuwa da kwanciyar hankali

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

  3. Daga Champioship zuwa Europa, Sunderland 2-1 Chelsea

    Duka magoya bayan Sunderland sun tashi cikin murna da farin ciki na yadda suka kai ga nasara a wasan da suka buga na kakarsu ta farko daga ɗagowa daga Premier bana.

    A bara ƙungiyar ta buga Championship, wadda sai da ta buga wasa sama da 10 ba a iya doke ta ba a gida.

    Yanzu ta samu tikitin zuwa gasar Europa, gasa ta biyu mafi daraja a nahiyar Turai.

  4. , Tottenham 1-0 Everton

    An kawo Roberto de Zerbi lokacin da ya rage saura wasa bakwai a gama Premier ga kuma firgicin faɗawa Champioship.

    Babu yabo babu fallasa, yayi nasara uku ya yi canjaras biyu, an kuma doke shi wasa biyu ya kuma dawo da ƙungiyar ta arewacin London Premier.

    Dan ƙasar Italiyan na da damar haɗa tawagar da yake so a kaka mai zuwa ya kuma yi gyaran da ya kamata a ƙungiyar.

  5. WEST HAM ta faɗa Champioship

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Komai ya ƙare bayan shekaru 14 da ta kwashe a Premier a ƙarshe West Ham ta koma Championship, gasar kwallon ƙafa ta Ingila mai daraja ta biyu.

    Hammers sun faɗa ne da maki 39 da suka iya haɗawa kacal a Premier bana.

    Tuni wasu magoya bayan ƙungiyar suka fice dga filin wasan na London, saboda zamansu a gasar ya ta'allaƙa ne da nasarar Everton a wasanta da Tottenham.

    Abin da suke tsoro ya afku.

  6. An tashi, Tottenham 1-0 Everton

    Tottenham ta tsallake rijiya da baya.

    Mogoya bayanta sun fara murna.

  7. An tashi, Nottingham Forest 1-1 Bournemouth

    Wasan Andoni Ariola na ƙarshe a Bournemouth, ya buga wasa 19 ba a yi nasara a kansa ba.

    Yanzu sun samu damar zuwa gasar Europa a kaka mai zuwa.

    b

    Asalin hoton, Getty Images

  8. An tashi, Sunderland 2-1 Chelsea

    Sunderland na da babban fata

  9. An tashi, Crystal Palace 1-2 Arsenal

    Masu kofi sun tashi suna ci gaba da murnar ɗaukar kofinsu.

  10. Tottenham na neman tsira

    Wasa na dab da ƙarewa kuma yana sake ɗaukar zafi.

  11. An tashi, West Ham 3-0 Leeds

    Damar da ke gaban West Ham na hannun Everton kuma Tottenham na iya ƙoƙarinta na tsira da kwallonta ɗaya.

  12. 🥅West Ham 3-0 Leeds

    Callum Wilson (90+4 mins)⚽️

    Ko kwallayen za su yi wa West Ham amfani,

    Yanzu suna jira su ji sakamakon wasan Tottenham domin sanin makomarsu.

  13. Ƙarin lokaci

    An kara minti 10 a wasan.

    Burin Brentford na Europa na dab da cika.

  14. Ana ta zubar da hawaye a Anfield

    A cire Mo Salah, wasansa na ƙarshe a ƙungiyar Liverpool.

    An shiga rudani a filin wasa na Anfield, magoya baya na ta zubar da hawaye.

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

  15. 🥅Crystal Palace 1-2 Arsenal

    Jean-Philippe Mateta (89 mins)⚽️

  16. 🥅Man City 2-2 Aston Villa

    Phil Foden (90+1 mins)⚽️

    Amma ana dubawa.

    VAR ta kashe kwallon

  17. Canji, Fulham 2-0 Newcastle

    Fulham ta yi canji:

    Shiga - Josh King, Harry Wilson, Tom Cairney, Raul JImenez.

    Fita - Kevin, Emile Smith Rowe, Oscar Bobb, Rodrigo Muniz.

  18. 🥅Fulham 2-0 Newcastle

    Tom Cairney (81 mins) ⚽️

  19. 🥅West Ham 2-0 Leeds

    Jarrod Bowen ⚽️

    Ko shakka babu West Ham na yunwar maki uku a wasan nan.

  20. Canji, Man City 1-2 Aston Villa

    Villa ta yi canji uku.

    Shiga: Amadou Onana, Youri Tielemans, Pau Torres.

    Fita: Lamare Bogarde, Douglas Luiz, Victor Lindelof.