'Iran ta daina kallon yarjejeniyar nukiliyarta da Amurka a matsayin mafita'

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon mai ba da shawara ga tsohon shugaban Amurka, Barack Obama, wato Vali Nasr, ya bayyana cewa Iran ta daina kallon yarjejeniyar nukiliyarta da Amurka a matsayin mafita ga matsalolinta na tattalin arziƙi da tsaro.
A wata maƙala da ya wallafa a jaridar Financial Times, Nasr ya ce Tehran na kallon wasu sassaucin ra'ayi da Amurka ke nunawa a tattaunawar da shakku, har ta kai ga ganin kamar ba za su zama gaskiya ba.
Nasr ya tunatar da cewa Iran tana da mummunar ƙwarewa daga yarjejeniyar nukiliya ta baya, inda shugaban Amurka Donald Trump ya janye ƙasarsa daga yarjejeniyar JCPOA. Ya kuma ce a lokacin tattaunawar da aka yi da Iran, gwamnatin Trump ta kai hare-hare sau biyu kan ƙasar, lamarin da ya ƙara rage amincewar Tehran ga duk wata sabuwar yarjejeniya.
Maƙalar da aka yi wa taken "Dalilin da ya sa Iran ta damu kan ko yarjejeniyar yau za ta zama yaƙin gobe" inda ya ce "Iran ta daina kallon yarjejeniyar nukuliyarta a matsayin mafitar matsalolinta ba"
Vali Nasr ya kuma bayyana cewa matsin lambar da Amurka ke yi na dakatar da Iran daga tace sinadarin uranium yana ƙara tabbatar wa Tehran cewa manufar Washington ita ce raunana ƙarfin kariyar Iran ta hanyar diflomasiyya kafin komawa ga amfani da ƙarfi.
Ya ce duk da cewa Amurka da Iran na iya cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen wannan rikici, samun wata yarjejeniya mai ɗorewa kan makomar Mashigar Hormuz da shirin nukiliyar Iran zai kasance babban ƙalubale.
A halin yanzu, ƙasashen biyu na ci gaba da tattaunawa inda Iran ke neman zaman lafiya mai ɗorewa, yayin da Amurka ke cewa manufarta ita ce tabbatar da cewa Iran ba ta mallaki makamin nukiliya ba.






















