Arsenal da Chelsea da Man U da Real Madrid na son Smit, Carrick na daf da zama kocin Man U

Kees Smit

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kees Smit
Lokacin karatu: Minti 2

Tottenham na kan gaba wajen neman dan wasan baya na hagu na Liverpool da Scotland, Andy Robertson mai shekaru 32, kyauta a bazara, idan har kungiyar ta Spurs ta kauce wa faduwa daga gasar bana. (Athletic)

Chelsea na iya sayar da dan wasan tsakiya na Argentina Enzo Fernandez a bazara idan har kungiyar ba ta samu tikitin shiga gasar Zakarun Turai ta kakar mai zuwa ba, inda ake alakanta dan wasan mai shekaru 25 da Real Madrid. (AS)

Manchester City ta gudanar da tattaunawa ta farko da Sporting kan daukar dan wasan tsakiya na Denmark, Morten Hjulmand mai shekaru 26, wanda kuma Manchester United da Juventus ke nema. (A Bola)

Dan wasan tsakiya na Atalanta Ederson ya ki amincewa da tayin kungiyoyi da suka hada da Arsenal, Manchester United da Newcastle, yayin da dan wasan Brazil mai shekaru 26 ke sha'awar komawa Atletico Madrid. (AS)

Arsenal, Chelsea, Liverpool, Manchester United, Newcastle, Barcelona da Real Madrid duk suna zawarcin dan wasan tsakiya na Netherlands da AZ Alkmaar, Kees Smit mai shekaru 20, a bazara. (CaughtOffside)

Manchester United, Arsenal, Chelsea da Paris St-Germain na duba yiwuwar daukar dan wasan gaba na Aston Villa da Ingila, Morgan Rogers mai shekaru 23, a bazara. (Sky Sports)

Arsenal ta yi cikakken nazari kan halin da dan wasan gefe na Ingila Anthony Gordon ke ciki a Newcastle, kuma tana sa ido kan yiwuwar samuwarsa kafin kasuwar bazara. (Teamtalk)

Celtic na shirin sayar da dan wasan gefe na Sweden Benjamin Nygren mai shekaru 24 a bazara, bayan sha'awar da Tottenham ta nuna, kuma ana sa ran fara tattaunawa kan kusan fam miliyan 26, yayin da Brighton, Bournemouth da Valencia suma ke sha'awa. (SportsBoom)

FC Cincinnati na duba hanyoyin daukar dan wasan gaba na Brazil Neymar mai shekaru 34 daga Santos zuwa gasar MLS, inda aka fara tattaunawa ta farko. (Athletic)

Mai horaswa na rikon kwarya Michael Carrick na kan gaba wajen zama cikakken kocin Manchester United, bayan tsohon dan wasan tsakiyar na Ingila mai shekaru 44 ya taimaka wa kungiyar samun maki 23 cikin 30 tun bayan da ya karbi ragamar aiki a watan Janairu. (Talksport)