Ko Najeriya ta shirya wa zuwan cutar Ebola?

...

Asalin hoton, AFP via Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

A baya-bayan nan Hukumar Daƙile Yaɗuwar Cututtuka a Najeriya, NCDC ta sanar da cewa duk da cewa babu rahoton ɓullar cutar Ebola a ƙasar daidai lokacin da ake ci gaba da samun bazuwar cutar a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo ƙasar na cikin shiri domin gudun abin da ke iya zuwa ya komo.

Bazuwar cutar na ƙara janyo fargaba a tsakanin sauran ƙasashen Afirka musamman ganin cewa Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta fito a kwanakin baya ta bayyana cewa zuwa yanzu babu allurar rigakafin nau'in cutar na 'Bundibugyo', wanda ya ɓulla a baya-bayan nan.

WHO ta ce za a ɗauki tsawon wata tara kafin samun allurar rigakafin cutar, wani lamari da zai ci gaba da haifar da fargaba da kuma tunanin rashin tabbas.

A cewar WHO, yawan mutanen da ake zargin sun kamu da cutar ya haura 900 sannan an tabbatar da mutuwar mutum 101 sakamakon cutar.

Matakan da NCDC ke ɗauka

..

Asalin hoton, Getty Images

A shafinta na X, hukumar NCDC ta duƙufa wajen faɗakar da mutane kan cutar ta Ebola inda ta ce galibi an fi samun cutar ta gumi ko kuma yin mu'amala da wanda ya kamu da ita.

NCDC ta bayyana wasu alamomin cutar da suka fi saurin bayyana kamar

  • Zazzaɓi
  • Ciwon kai
  • Kasala
  • Ciwon jiki
  • Amai
  • Gudawa
  • Fitar jini

NCDC ta ce ta ƙarfafa matakan sa ido tare da tanadar ɗakunan gwaje-gwaje da hana yaɗuwar cutar sai kuma ƙara himma wajen faɗakar da mutane a sassan ƙasar.

Hukumar ta shawarci ƴan Najeriya da su kwantar da hankalinsu su kuma yawaita tsaftace hannayensu, su guji yaɗa labarai marasa tushe sannan kuma su gaggauta zuwa asibiti da zarar sun ji jikinsu babu daɗi.

A cewar NCDC, sakamakon ƙaruwar tafiye-tafiye a nahiyar Afirka, tana ƙara bibiyar lamarin tare da yin aiki da masu ruwa da tsaki don tabbatar da cewa an zama cikin shirin ko ta kwana ko da an samu ɓullar cutar.

Abin da ya kamata ƙasashen Afirka su yi

Farfesa Abdulsalam Nasidi, ƙwararre kan ƙwayoyin cututtuka ya shaida wa BBC cewa Ebola cuta ce mai saurin yaɗuwa a don haka akwai buƙatar ƙasashen Afirka su kare kansu daga ɓullar cutar musamman saboda rashin samun allurar rigakafinta nan kusa.

Ya ce daga cikin matakan da ƙasashen Afirka ya kamata su ɗauka akwai ƙarfafa ɓangaren lafiyarsu ta yadda za su iya saurin gano baƙuwar cuta.

Ya kuma buƙaci su nemo magungunan da za su iya warkar da waɗanda suka kamu da cutar sannan a ƙarfafa ɗakunan gwaje-gwaje ta yadda za a yi saurin gano cutar ko da ta ɓulla.

A cewar shi, abin tayar da hankali kan bazuwar cutar a yanzu musamman a Congo shi ne ta ɓulla a ƙasar amma ba a farga ba har sai bayan wajen mako biyu zuwa uku.

Me ya janyo jan ƙafa wajen samun rigakafi?

Masanin ya ce "ƙwayoyi shida ne suke janyo cututtuka a jikin mutum, guda huɗu sun fi tsanani, kuma irin ƙwayar da ke janyo Bundibugyo tana yin tsanani a jikin mutum fiye da waɗanda aka sani a baya." in ji shi.

Ya ce magungunan da ake da su a baya da kuma allurar rigakafin ba a tunanin za su taimaka wajen magance nau'in Ebola na yanzu.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ana ƙoƙarin samar da rigakafin da za a yi gwaji da su. Ta kuma ce akwai yiwuwar allurar rigakafin da aka samar lokacin da aka samu nau'in cutar na Zaire ya samar da kariya ta wucen gadi.