Man City da Chelsea na son Cambiaso, Barca za ta riƙe Rashford

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City da Chelsea na son dan baya na gefe na Juventus Andrea Cambiaso, kamar yadda ita ma Barcelona ke sa ido a kan dan tawagar ta Italiya mai shekara 26. (Gazzetta dello Sport)
Kungiyoyin Bayern Munich da Arsenal na sha'awar sayen dan bayan Eintracht Frankfurt ta Jamus Nathaniel Brown, mai shekara 22. (The Athletic)
Aston Villa na sane da sha'awar da kungiyoyi da dama ke nunawa a kan danwasanta na tsakiya Morgan Rogers. Kungiyoyin da suka hada da Arsenal, amma kuma ba ta da niyyar sayar da danwasan na tawagar Ingila mai shekara 23. (Telegraph)
Watakila Liverpool da Paris St-Germain su nemi sayen danwasan gaba na gefe na RB Leipzig Yan Diomande amma kuma kungiyar ta Jamus ba ta nuna wata damuwa ba a kan lamarin kasancewar ta yi amanna matashin mai shekara 19, ba kawai zai so ya kara shekara daya ba a kungiyar, zai ma rattaba hannu a kwan wani sabon kwantiragin da ya fi na da armashi. (Sky Sports)
Kociyan Barcelona Hansi Flick, da darektan wasanni Deco da kuma shugaban kungiyar Joan Laporta har yanzu suna sha'awar rike dan gaban Manchester United Marcus Rashford da ke zaman aro a kungiyar ya zama na dindindin, yayin da Bayern Munich, da Newcastle, da Tottenham da kuma Aston Villa ke nuna sha'awarsu a kan dan tawagar ta Ingila mai shekara 28. (The I)
Juventus na duba yuwuwar sayen dan gaban Bournemouth da tawagar Netherlands Justin Kluivert mai shekara 27, a madadin Brahim Diaz na Real Madrid da Morocco, mai shekara 26. (Gazzetta dello Sport)
Manchester United na zawarcin dan bayan Juventus da Faransa Pierre Kalulu, kuma kila kungiyar ta Italiya ta sayar da danwasan mai shekara 25, bayan da ta kasa samun gurbin zuwa gasar Zakarun Turai. (Corriere dello Sport)
An bai wa danwasan tsakiya na Portugal Mateus Fernandes, mai shekara 21, damar barin West Ham bayan Manchester United da Arsenal, sun yi tuntuba a kansa, yayin da ita ma Liverpool da Paris St-Germain suna sa ido a kan makomarsa. (Teamtalk)
Aston Villa, da Atletico Madrid da Borussia Dortmund na sha'awar dan gaban Club Brugge, na Jamus Nicolo Tresoldi, mai shekara 21, bayan tashen da ya yi a Belgium a kakar da ta kare. (The Athletic)
Real Madrid ta tattauna da dan bayan Inter Milan Denzel Dumfries, wanda kwantiraginsa ya tanadi sayar da shi a kan fam miliyan 21.6, a yunkurin da kungiyar ta Sifaniya ke yi na ganin ta sayi dan tawagar Netherlands mai shekara 30 a matsayin babban wanda za su saya domin karfafa bayansu. (Athletic)














